Connect with us

News

An Gano Bindiga A Gidan Wanda Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta gano bindiga kirar AK-47 ta bogi a gidan ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kisan DPO na Rano, CSP Baba Ali.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Advertisement

FASAHAR ZAMANI DA KARATUN LITTATTAFAI: Masana Sun Fadi Yadda Fasahar Zamani Ke Rage Sha’awar Karatu

A cewarsa, an gano bindigar ce yayin wani samame da jami’an tsaro suka kai a gidan ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a wannan ta’asa. Ya ce bindigar kirar AK-47 ce, amma ta bogi, kuma ana zargin tana da alaƙa da kisan DPO ɗin.

A makon da ya gabata ne wasu matasa suka kai hari ofishin ’yan sanda na Rano, inda suka hallaka DPO na ofishin, CSP Baba Ali, yayin da yake bakin aiki. Harin ya jawo asarar rayuka da jikkatar wasu, tare da kona wani ɓangare na ofishin.

Advertisement

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa bincike ya na ci gaba, tare da ƙudurin zakulo duk masu hannu a lamarin domin su fuskanci hukunci.

SP Kiyawa ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai da bayanai domin kawo ƙarshen aikata laifuka a cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending