Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Fara Horos Da Masu Ɗauko Rahotannin Ayyuka A Ma’aikatu SR /SSR ‎

Published

on

0 0x0 0 0#

Gwamnatin Jihar Kano ta fara horas da Masu Ɗauko Rahotannin Ayyukan Gwamnati (SR) da Manyan Masu Rahoto (SSR) domin ƙarfafa sadarwa da kuma inganta isar da manufofi da nasarorin gwamnati ga al’umma.

‎An bude horon ne a ranar Litinin, ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Aikin Jarida ta Ƙasa (IIJ) da Kamfanin AUSAM Communication, wanda zai gudana na tsawon kwanaki huɗu.

Advertisement

Kotu Ta Tsare Likita Mai Shekaru 72 Bisa Zargin Satar Yaro Da Siyar Da Shi 

‎Taken horon shi ne: “Sabunta Dabarun Sadarwar Jama’a Don Inganta Huldar Gwamnati da Al’umma.”

‎Kwamishinan Ma’aikatar, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa wakilan SR da SSR su samu sabbin dabaru da ƙwarewa a fannin yada sahihan bayanai kan ayyukan gwamnati.

Advertisement

‎Ya ce kafin wannan lokaci, gwamnati ta gudanar da irin wannan horo ga jami’an yada labarai na kananan hukumomi, domin tabbatar da cewa duk matakin gwamnati na da wakilin da ke isar da bayani cikin gaskiya da inganci.

‎Shugaban Ma’aikata na jihar Kano, Malam Abdullahi Musa, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron, ya ce shirin kafa SR da SSR wani sabon salo ne da aka ƙirƙiro don samar da ingantaccen tsarin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.

Advertisement

‎Ya bukaci mahalarta horon da su kasance masu gaskiya, kwarewa da kuma bin ƙa’idojin aikin jarida wajen isar da rahotannin ayyukan gwamnati.

Advertisement

‎Shi kuwa Shugaban Ƙungiyar SR da SSR, Amir Abdullahi Kima, ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewar da yake nunawa wajen ƙara wa ma’aikatan gwamnati ilimi da ƙwarewa a fannin yada labarai.

‎Binciken da Indaranka ta yi ya nuna cewa kwararrun malamai daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) ne za su jagoranci wannan horo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending