Labarai
Gwamnatin Kano Ta Fara Horos Da Masu Ɗauko Rahotannin Ayyuka A Ma’aikatu SR /SSR

Gwamnatin Jihar Kano ta fara horas da Masu Ɗauko Rahotannin Ayyukan Gwamnati (SR) da Manyan Masu Rahoto (SSR) domin ƙarfafa sadarwa da kuma inganta isar da manufofi da nasarorin gwamnati ga al’umma.
An bude horon ne a ranar Litinin, ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Aikin Jarida ta Ƙasa (IIJ) da Kamfanin AUSAM Communication, wanda zai gudana na tsawon kwanaki huɗu.
Kotu Ta Tsare Likita Mai Shekaru 72 Bisa Zargin Satar Yaro Da Siyar Da Shi
Taken horon shi ne: “Sabunta Dabarun Sadarwar Jama’a Don Inganta Huldar Gwamnati da Al’umma.”
Kwamishinan Ma’aikatar, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa wakilan SR da SSR su samu sabbin dabaru da ƙwarewa a fannin yada sahihan bayanai kan ayyukan gwamnati.
Ya ce kafin wannan lokaci, gwamnati ta gudanar da irin wannan horo ga jami’an yada labarai na kananan hukumomi, domin tabbatar da cewa duk matakin gwamnati na da wakilin da ke isar da bayani cikin gaskiya da inganci.
Shugaban Ma’aikata na jihar Kano, Malam Abdullahi Musa, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron, ya ce shirin kafa SR da SSR wani sabon salo ne da aka ƙirƙiro don samar da ingantaccen tsarin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya bukaci mahalarta horon da su kasance masu gaskiya, kwarewa da kuma bin ƙa’idojin aikin jarida wajen isar da rahotannin ayyukan gwamnati.
Shi kuwa Shugaban Ƙungiyar SR da SSR, Amir Abdullahi Kima, ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewar da yake nunawa wajen ƙara wa ma’aikatan gwamnati ilimi da ƙwarewa a fannin yada labarai.
Binciken da Indaranka ta yi ya nuna cewa kwararrun malamai daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) ne za su jagoranci wannan horo.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
