Connect with us

News

Rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Najeriya — Imam Murtadha Gusau

Published

on

1753422562209 9mrstl 170914078eefd21525efc29189bef403ff29f33e91413f9f65257f0fcdf98d82

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’un.

Al’ummar jihar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya na cikin jimami sakamakon rasuwar Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Dr. Ibrahim Bello, wanda Allah Ya karɓi rayuwarsa a safiyar ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025, bayan gajeruwar rashin lafiya a babban birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Marigayin Sarki ya rasu yana da shekara 71 a duniya, ya bar mata da ’ya’ya, jikoki da dumbin iyalai da abokan arziki.

Sarkin Katsinan Gusau, Dakta Ibrahim Bello ya rasu

Rasuwar tasa ta bar babban gibi da zai ɗauki dogon lokaci kafin a cike shi a masarautar Gusau da jihar Zamfara da kuma arewacin Najeriya, ganin yadda ya shafe shekaru goma yana jagorantar al’umma da kishin ci gaban kasa da mutunta kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Advertisement

Sarkin ya hau kujerar mulki ne a ranar 16 ga Maris, 2015, kuma shi ne Sarki na 15 da ya shugabanci masarautar Gusau. A baya kafin ya zama Sarki, ya rike mukaman gwamnati a jihohin Sokoto da Zamfara, inda ya kai matakin Babban Sakatare. Ya kasance jagora nagari mai rikon amana, hangen nesa, da sadaukarwa wajen ganin al’umma sun samu ci gaba.

A cewar Imam Murtadha Gusau, “Marigayin ya kasance mutum mai gaskiya, mai karimci, jajirtacce, mai tausayi da juriya. Irin waɗannan halaye suka sanya ya samu gagarumin girmamawa a wajen al’umma.”

Advertisement

Imam Murtadha ya mika sakon ta’aziyya zuwa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Shugaban Ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal; da iyalan marigayin da kuma dukkan al’ummar jihar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma bayyana cewar haduwarsa ta ƙarshe da Marigayin Sarki ita ce bayan sallar Juma’a a masallacin Rabi’ah da ke Gusau, lokacin da aka daura auren diyar yayarsa. “Mun yi musabaha da gaisuwa. Ya ce Imam, ashe kana nan? Saboda mun dade bamu haɗu ba. Muka yi sallama, ban san shi ne karo na ƙarshe da zan gan shi da ido ba,” inji Imam Murtadha.

Advertisement

Za a gudanar da sallar jana’izar marigayin Sarki da misalin ƙarfe 2:30 na rana, bayan sallar Juma’a, a Babban Masallacin Juma’a da ke kusa da fadar Sarki a Gusau. Hukuma za ta sanar da sauyin lokaci idan akwai.

Imam Murtadha ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Marigayin, Ya yaye masa zunubai, Ya sa Aljannah Firdausi ta kasance makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar Zamfara da Musulmi baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi.

Advertisement

“Mun yi rashin uba, shugaba, da jagora. Allah Ya jikan shi da rahama, Ya sanya mu daga cikin waɗanda zamu yi koyi da kyawawan halayensa,” in ji Imam Murtadha.

 

Advertisement

Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi. Za a iya tunt

ubarsa ta lambar waya: 08038289761.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending