News
An Kama Budurwa Mai Shekara 19 Kan Zargin Ajalin Yara Biyu A Bauchi
Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wata budurwa mai shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace wasu yara mata biyu da kuma kashe su a wata gona da ke cikin daji.
Kakakin rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne ranar 22 ga watan Yuli, 2025, a ƙauyen Unguwar Sarkin Yaki da ke karamar hukumar Toro.
Rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Najeriya — Imam Murtadha Gusau
Yara da lamarin ya shafa sun hada da Khadija Sama’ila da A’isha Dahiru – dukkansu ’yan shekara bakwai.
A cewar ’yan sanda, wacce ake zargin ta yaudari yaran ne ta tafi da su zuwa daji, inda daga bisani ta kashe su da adda a wata gona da aka dasa masara.
Wakil ya ce rundunar ta samu rahoton ne da misalin karfe 3 na rana, kuma cikin gaggawa suka hada gwiwa da ’yan banga wajen gudanar da bincike da farauto wacce ake zargin.
A yayin bincike, an gano gawarwakin yaran kuma an ceto wata jaririyar da ake zargin an sace tare da su.
Rahoton farko ya nuna cewa Esther ta aikata laifin ne domin ta samu jaririya da za ta mikawa wata mata mai suna Nafisa Dahiru.
Bayan da ta samu jaririyar, sai ta kaisu cikin daji inda ta kashe yaran biyu kafin ta gudu.
Bayan da aka gano gawarwakin yaran, tashin hankali ya barke a yankin, inda matasa suka gudanar da zanga-zanga, har da kona wasu coci da yunkurin kona ofishin ’yan sanda a garin Tulu.
CSP Wakil ya ce jami’an tsaro sun daƙile lamarin bayan tura ƙarin runduna daga sassan da ke kusa, kuma sun kama mutane 16 da ake zargi da hannu a tarzomar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ce za a ci gaba da bincike domin gano duk wadanda ke da hannu a lamarin, tare da shan alwashin tabbatar da doka da oda.
