Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Babban Mai Safarar Ƙwayoyi , Ta Lalata Wiwi Sama Da Kilo Dubu 37 

Published

on

1755451353567

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wani sanannen mai safarar miyagun ƙwayoyi, Sunday Ibigide, tare da abokin harkallarsa Clement Osuya a Asaba, jihar Delta.

‎Rahoton hukumar ya bayyana cewa an kama su ne da ƙunshin ƙwayar skunk 250 mai nauyin kilo 138, a cikin wata mota da suka tanada domin rabawa dillalan su.

Advertisement

Dalilan Ayya­na Zaɓen Cike Gurbi A Zamfara A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba —INEC

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce an shafe sama da shekaru uku ana neman Ibigide tun bayan da aka gano hannunsa a wata harkalla a ranar 19 ga Maris, 2022, inda aka kama kilo 24.137 na ƙwayoyi.

‎Ya ƙara da cewa NDLEA ta gudanar da bincike mai zurfi a jihohi daban-daban, wanda ya kai ga cafke masu hannu da yawa a safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

‎A wani samame da jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar sojoji da ’yan banga suka kai a Enugu Ezike, Jihar Enugu, an gano da kuma lalata kimanin kilo dubu 37,500 na wiwi a gonaki masu fadin hektoci 15.

‎Babafemi ya ce a yayin wannan samame an kama mutane shida da ake zargi da hannu a cikin haramtacciyar harka.

Advertisement

‎Masu hannu a wannan harkalla sun haɗa da ,Ugwuanyi Chinaso (23), James Negedu (26), Sopuruchukwu Obido (22), Ebuka Onu (30), Ukwueze Sunday (42) da Oguche Friday.

‎Hukumar ta ce an kuma kwato ƙarin kilo 74.5 na miyagun ƙwayoyi, kuma za a gurfanar da su a kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending