News
Tallafin Barau Ya Ƙara Ɗaga Darajar Ci Gaban BUK – Shugaban Jami’ar
Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, ya bayyana jin daɗin jami’ar bisa tallafin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibril, ya bayar domin ci gaban makarantar.
Farfesa Musa ya yi wannan jawabi ne a Abuja lokacin da ya kai wa Sanata Barau ziyarar ban-girma a majalisar dokoki.
Jami’an ‘yan Sanda Sun Kama Sojan Bogi Da Masu Satar Mota Uku A Jigawa
Ya ce jami’ar ta yaba da ƙudirin Sanatan na sabunta filin wasan kwallon ƙafa da ke sabuwar harabar jami’ar.
“Wannan aiki ya nuna sadaukarwa da kishin al’umma. Haka kuma al’umma za su ci gajiya da wannan ƙoƙari,” in ji Farfesa Musa.
Shugaban jami’ar ya ƙara da cewa suna yi wa Sanatan fatan Allah ya saka masa da alkairi tare da kuma albarka mai dorewa.
