Connect with us

Business

‎Kasuwa – Patake Caravan Ta Ƙaddamar Da Sabon Dandamali Na Kasuwancin Dabbobi A Najeriya

Published

on

IMG 20250924 WA0011
Spread the love

Kamfanin Kasuwa – Patake Caravan Digital Livestock Market ya ƙaddamar da sabon dandamali na zamani da ke nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci, tallata dabbobi da kuma ƙarfafa ƙungiyoyi da ’yan kasuwa a fadin Najeriya.

‎A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce an gina dandamalin ne domin haɗa masana’antu, ƙungiyoyi da kuma masu zaman kansu a wuri guda, tare da samar musu da sabis na kasuwanci da fasahar zamani cikin sauƙi.

Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Mutum Biyu A Kaduna

‎POS kyauta da kayan ofis ga masu rajista

‎Kamfanin ya bayyana cewa duk wanda ya yi rajista da kuɗi ₦2,500 zai samu na’urar POS kyauta, tare da muhimman kayan aikin ofis don farawa.

Advertisement

‎Kayan ofis ɗin sun haɗa da ,Takardun Letterhead, ‎Katin kasuwanci (Business Cards), ‎Invoices, Waybills da Receipts.

Sauran takardun gudanar da kasuwanci

‎Kamfanin ya ce wannan tallafi zai taimaka wajen rage kuɗin gudanarwa da kuma ƙarfafa martabar harkokin kasuwanci na mambobi.

‎Tallafin ayyukan kasuwanci

Advertisement

‎A matsayin wani ɓangare na tsarin haɗin gwiwa, dandamalin zai ba mambobi damar amfani da muhimman sabis na kasuwanci kamar

‎Rijistar kasuwanci (CAC), Annual Returns da Tax Clearance, Sabunta rajistar mota da inshorar kasuwanci, Talla ta hanyar kafafen sada zumunta

‎Haka kuma, akwai sabis na CBHI wanda ke samar da inshorar lafiya mai araha ga mutum, iyali ko ƙungiya, da CIP wanda ke ba da damar ajo da lamuni mai juyawa.

‎Haka zalika, SLS zai samar da taimakon lauya kan harkokin haya, kwangila da wakilci a kotu.

Advertisement

‎Sabbin shirye-shirye na kasuwa

‎Kamfanin ya ce yayin da dandamalin ke ƙara samun mambobi, zai ƙaddamar da wasu sabbin shirye-shirye da suka haɗa da , ‎Patake Spot Market: Kasuwar sati ta dabbobi, Digital Bargains Market: Shinikin dabbobi da tseren tayi, Patake Auctions Market: Gwanjon dabbobi, BNPL Animal Deals: Saya yanzu, biya daga baya, Business & Family Support Card: Tallafi ga kasuwanci da iyali.

‎AIKA-NG Blockchain & Express: Isar da dabbobi kai tsaye ga masu siya.

Advertisement

‎“Muna son sauya yadda ake kasuwanci a Najeriya”

‎Manajan shirye-shirye na kamfanin a Kano, Abdu Ado, ya ce manufar wannan dandamali ita ce sauya yadda ake gudanar da kasuwanci a fannin dabbobi ta hanyar fasahar zamani.

‎ “Muna son sauya fasalin harkokin kasuwanci a Najeriya domin baiwa mutane damar yin kasuwanci cikin sauƙi, tsari da kuma ƙarin fa’ida,” in ji shi.

‎Ya ƙara da cewa tawagar kamfanin za ta yi aiki tare da ƙungiyoyi domin kafa ofishin bayar da sabis a wuraren su, don tabbatar da cewa mambobi suna samun dukkan ayyukan cikin sauƙi da sauri.

Advertisement

‎Masu sha’awar shiga tsarin ko neman ƙarin bayani za su iya tuntuɓar kamfanin ta wayar 0803 303 3694, 0814 389 2963 ko 0806 816 0763.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *