Connect with us

News

Jami’an ’Yan sanda sun kama mutum 4,383, sun ceto 1,138 daga hannun masu garkuwa cikin watanni uku

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 4,383 tare da ceto mutane 1,138 da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar cikin watanni uku da suka gabata – daga 31 ga watan Yuli zuwa 23 ga Satumba, 2025.

Sufeto Janar na ’Yan sanda, Kayode Egbetokun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce cikin waɗanda aka kama akwai 481 da ake zargi da fashi da makami, 260 da satar mutane, 371 da kisan kai, 161 da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, da kuma 322 da ake zargi da fyade.

Advertisement

Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Mutum Biyu A Kaduna

Egbetokun ya ce jami’an rundunar sun kuma ƙwato bindigogi 716, harsashi sama da 21,000, da kuma motocin sata 212 a lokacin da suke gudanar da samame a sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma, ya ce ’yan sanda sun lalata sansanonin kungiyar IPOB da ESN a Kudu maso Gabas tare da kama wasu da ake zargi da aikata laifuka a jihohin Edo, Delta, Ogun da Zamfara.

Advertisement

Sufeto Janar ya ja hankalin kwamandojin ’yan sanda a jihohi da su fi mai da hankali wajen goyon bayan al’umma da tabbatar da bin doka da oda, yana mai cewa amincewar jama’a ita ce ginshikin nasarar rundunar.

“Shugabancin rundunar ya kuduri aniyar amfani da sabbin dabaru, ƙwarewar aiki, da ƙarfafa haɗin kai da al’umma domin rage laifuka da tabbatar da tsaro a duk faɗin ƙasar,” in ji Egbetokun.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending