News
Tankar Mai Ɗauke Da Lita 60,000 Na Man Fetur Ta Fadi
Wata tankar mai ɗauke da lita 60,000 na man fetur ta fadi a garin Iroko, da ke kan hanyar Oyo zuwa Ibadan, a ranar Lahadi da yamma, lamarin da ya haifar da zubewar danyen mai a hanya.
Rahotanni sun ce tankar mai lambar rajista GZA 55OXA ta karkata zuwa cikin rami a gefen hanya, inda man da take ɗauke da shi ya zube.
’Yan Fashi Sun Kwashi Kayan Tarihi Masu Tsadar Gaske A Gidan Tarihi Na Paris Cikin Mintuna Hudu
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Maroof Akinwande, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu wanda ya jikkata ko ya rasa ransa.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tunawa da wani hatsarin tankar mai da ya faru ‘yan kwanaki da suka gabata a yankin Ogbomoso na jihar, wanda ya haddasa cunkoso da fargaba a tsakanin jama’a.
