Connect with us

News

Wasu ‘yan daba sun banka wa hedikwatar ADC a Ekiti wuta

Published

on

ADC

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun cinna wuta ga sakatariyar jam’iyyar ADC da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, a daidai lokacin da ake shirin kaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar.

Wutar ta lalata kadarori da dama ciki har da tantin da ke daukar mutum 1000 da kujerunsa, da kuma wani bangare na ginin sakatariyar da aka banka wa wuta.

‎Tankar Mai Ɗauke Da Lita 60,000 Na Man Fetur Ta Fadi  ‎

Mambobin jam’iyyar ADC sun yi Allah-wadai da harin, suna kuma kira ga hukumomin tsaro da su binciko wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da gurfanar da su a gaban doka.

A halin yanzu, magoya bayan jam’iyyar sun taru a hanyar Basiri inda sakatariyar ta ke, suna jiran zuwan jagororin jam’iyyar na kasa da za su kaddamar da sabbin shugabannin.

 

 

Advertisement

TRUST RADIO 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending