News
Gwamnatin Katsina Ta Fara Rushe Shagunan Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Gwamnatin Jihar Katsina ta fara rushe shagunan jama’a da aka gina a gefen tituna da kuma kusa da gine-ginen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba a cikin birnin Katsina.
Hukumar Tsara Birane da Gundumomi ta jihar (URPB) ce ke gudanar da aikin, da nufin tabbatar da bin ƙa’idojin gine-gine da kare muhalli da lafiyar jama’a.
Wuraren da aka fara da su sun haɗa da shatatalen High Court zuwa hanyar Daura, titun Sarki Abdulrahman, da kwaran High Court, tare da wasu muhimman sassan cikin birnin Katsina.
Wasu daga cikin masu shagunan da aka rusa sun bayyana rashin jin daɗi, inda suka zargi hukumomin da rashin bayar da isasshen lokaci ko damar gyarawa kafin rushe shagunan nasu.
Sai dai hukumar URPB ta ce aikin ba zai tsaya ba, har sai an share duk wuraren da aka gina ba bisa ƙa’ida ba, domin inganta kyawun birnin da tabbatar da tsaro da tsaftar muhalli.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News18 hours ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
