News
Fashewar Tankar Man Fetur Ta Hallaka Akalla Mutum 30 A Neja
Mutane akalla 30 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 40 suka jikkata a sakamakon fashewar wata tankar mai ɗauke da fetur a kan hanyar Agaie–Baddegi da ke jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Essa, dab da Agaie, da misalin ƙarfe 11 na safiyar Talata, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa LEADSHIP HAUSA
Gwamnatin Katsina Ta Fara Rushe Shagunan Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Wani mazaunin garin da ya ga yadda abin ya faru ya ce, “Tankar man ta yi hatsari ne tana sauka daga kan tudu, ta bugu da wata mota, nan take ta zube man fetur. Wasu matasa suka ruga domin kwaso man, sai kawai abin ya kama da wuta.”
Shaidu sun ce wutar ta bazu da sauri, inda ta kama motocin dake kusa da wajen, tare da kone mutane da yawa da ke kusa.
Shugaban Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai ta Jihar Neja (PTD), Kwamared Farouk Mohammed Kawo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumomin kashe gobara da jami’an tsaro sun isa wurin domin taimakawa wajen kashe wutar da kuma ceto mutane.
Kwamared Kawo ya ce, “Lamarin abin takaici ne sosai. Da yawa daga cikin waɗanda suka mutu ba direbobi ba ne, amma jama’ar gari da suka yi gaggawar zuwa wajen don su kwaso man fetur.”
A halin da ake ciki, hukumomi sun rufe hanyar Agaie–Baddegi na ɗan lokaci, yayin da ake ci gaba da bincike kan ainihin musabbabin hatsarin.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News13 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
