Connect with us

News

Wani Matashi Ya Ƙwaƙwule Idon Kanwar Sa Yar Shekara 7 A Bauchi

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta cafke wani matashi da boka, bayan aikata mummunan laifi da ya girgiza ƙauyen Wailo, ƙaramar hukumar Ganjuwa.

Auwalu, matashin da ake zargi, ya ja kanwarsa mai shekaru 7 cikin daji, inda ya ƙwaƙwule mata idanuwanta domin biyan bukatarsa ta duniya.

Ashraf Mahrous Jarumin Ya Ja Jirgi Mai Nauyin Tan 700 Da Haƙoransa

Mahaifin yarinyar, Malam Muhammad Adamu, ya bayyana cewa ɗan uwansa ne na jini, amma ya ci amanarsu ta hanyar yaudarar yarinyar kafin aikata wannan ta’annati.

“Ya ja kanwarsa cikin daji, ya aikata wannan mummunan aiki. Idanun ta biyu sun jikkata sosai,” in ji Malam Muhammad.

An gaggauta daukar Ruƙayya zuwa Asibitin Koyarwa na ATBUTH, inda likitocin ido suka yi ƙoƙarin gyara raunukan. Sai dai Babban Likitan Ido na ATBUTH, Dr. Shahir Bello Umar, ya bayyana cewa ganin yarinyar ba zai dawo ba, saboda lalacewar idanuwanta biyu.

Wani shaidar gani da ido wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya tabbatar wa Jaridar  The Stantorn news cewa, jami’an tsaro sun cafke Auwalu da boka da ya taimaka masa wajen samun idon domin yin tsafi.

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sanda, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da lamarin, yayin da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Omolarin Aliyu, ya bayar da umarnin ci gaba da bincike domin gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending