Connect with us

News

‎Ƴansanda Sun Kama Wani Dattijo Mai Shekara 63, Bisa Zargin Satar Babur A Neja.

Published

on

Rundunar Ƴansanda ta jihar Neja ta kama wani dattijo mai shekara 63, bisa zargin satar babur kirar Bajaj a ƙauyen Tugan-Kawo da ke cikin ƙaramar hukumar Kontagora.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an cafke shi ne a lokacin da ya ke ƙoƙarin satar babur ɗin, inda jami’an tsaro suka same shi da makullai da dama da ake zargin yana amfani da su wajen buɗe babura.

Advertisement

Wani Matashi Ya Ƙwaƙwule Idon Kanwar Sa Yar Shekara 7 A Bauchi

‎Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa an kama wanda ake zargin ne tare da taimakon ƴan banga.

‎Abiodun ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan kama shi, kuma daga baya an gano mamallakin babur ɗin da aka yi ƙoƙarin satarwa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending