News
Mai Wushirya ya fasa auren Yar Guda
Fitaccen ɗan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya bayyana cewa ba zai auri Basira ’Yar Guda da kotu ta umarce shi bayan tuhumarsa da wasu laifukan watsa baɗala a kafafen sada zumunta.
Cikin wani sabon bidiyo da Mai Wushirya ya fitar, ya bayyana cewa duba da ƙorafe-ƙorafen da iyayensa suka yi da sauran abokansa, yana shaida wa mutane cewa idan ya tashi aure zai sanar da su.
Ya ƙara da cewa da ma ba a son ransa ya amsa cewa zai auri ’yar Guda ba, tsoro ne na hukuncin kotu.
A ƙarshe ya ce yana kira da duk waɗanda suka karɓi kuɗin gudunmawa da sunan wannan biki da su kai kuɗin ga mabuƙata da marayu.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
