Connect with us

News

Wani Saurayi Ya Kashe Abokinsa Saboda Rikici Kan Budurwa

Published

on

Unguwa gawa

Wani saurayi mai shekaru 25, Hammed Usman Tunde, ya rasu bayan abokinsa, Gafar mai shekaru 21, ya soka masa wuƙa a kirji. Lamarin ya faru ne a unguwar Oja Gboro, babban birnin jihar Kwara, sakamakon rikici da suka yi kan wata budurwa.

Rahotanni daga wurin sun bayyana cewa rikicin ya fara ne a wajen mai sayar da rake, inda suka fara muhawara wadda ta kai ga tashin hankali. A lokacin, Gafar ya caka wa Tunde wuƙa a kirji.

Advertisement

Kwamishinan Shari’a Na Kano Ya Halarci Taron Nahiyar Afrika Kan Yaƙi Da Safarar Mutane A Legas

An garzaya da Tunde asibiti, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. Mamacin ya kasance mazaunin Ile-Soro 2, Isale Koko, Oja Gboro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending