News
WAEC Ta Fara Gwajin Rubuta Jarabawar ‘Essay’ Ta Kwamfuta Kafin 2026
Hukumar jarrabawar Afirka ta Yamma, WAEC, ta gudanar da gwajin rubuta essay ta kwamfuta a wani shiri na shiryawa jarabawar ta kwamfuta gaba daya (Computer-Based WASSCE) da za a fara a shekarar 2026.
An gudanar da gwajin ne a Cibiyar Horarwa da Gwaji ta WAEC da ke Ogba, Legas, karkashin jagorancin shugaban ofishin hukumar a Najeriya, Dr. Amos Dangut.
Daliban makarantun sakandare na gaba da sakandare ne suka halarci gwajin domin sabawa da tsarin sabon salo na jarrabawar da zai haɗa tambayoyin objective da essay a kwamfuta.
Dangut ya bayyana cewa manufar gwajin ita ce shirya ɗalibai da makarantun Najeriya su rungumi jarrabawar ta hanyar amfani da fasahar zamani, da kuma rage gibin fasaha tsakanin makarantun birane da karkara.
Advertisements
