News
China Ta Gargadi Amurka Kan Tsoma Baki Cikin Harkokin Najeriya
Gwamnatin China ta yi gargadi ga Amurka kan duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya, bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na amfani da sojoji don hukunta Najeriya kan zargin cin zarafin Kiristoci.
A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, ya bayyana cewa Beijing “na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu gaba ɗaya wajen tafiyar da al’amuran Najeriya a kan hanya madaidaiciya da ci gaba.”
Jami’an NSCDC Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Kan Hanyar Zariya–Kano
Mao ya kara da cewa:”China, a matsayin ta na abokiyar haɗin gwiwa, tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko hujjar kare haƙƙin ɗan adam wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida, ko yin barazanar takunkumi ko amfani da ƙarfi.”
Wannan martani na China ya biyo bayan damuwar da maganganun Trump suka haifar a fadin Afirka da sauran sassan duniya, inda ƙasashe da dama suka yi Allah wadai da barazanar Amurka.
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
