News
Jami’an NSCDC Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Kan Hanyar Zariya–Kano
Rundunar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi, da kuma haɗa baki wajen aikata laifuka a kan hanyar Zariya zuwa Kano, da ke tsakanin jihohin Kaduna da Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSC Afolabi Babawale, ya fitar daga babban ofishin NSCDC na ƙasa a Abuja, ya ce rundunar ta kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga jami’an leƙen asiri, inda Rukuni na Musamman na Leƙen Asiri ƙarƙashin jagorancin Commandant A. S. Dandaura (JP) ya gudanar da samame a yankin.
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jikkata ‘Yan Sanda Biyu Da Jami’in NSCDC A Yobe
An gano cewa waɗanda aka kama sun haɗa da Ibrahim Abubakar Garba, Umar Fulani, Aliyu Mohammed, Murtala Salisu, da Imrana Hassan — dukkansu maza ne, kuma sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi bayan kama su.
A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su, Sani Ahmad, ya bayyana cewa shi ɗan jarida ne da ke tafiya daga Zariya zuwa Kano a lokacin da lamarin ya faru. Ya ce wasu mutane sun tsayar da motarsa suna cewa akwai haɗari a gaba, amma daga bisani suka afka masa suka kwace kayayyaki da kuma kuɗin sa.
>“Da suka tsayar da ni, sai suka shiga cikin motar suka karɓe jakata, suka kwace waya ta iPhone 12 Pro Max guda biyu, Tecno Camon 40 Pro, sannan suka tilasta mini in tura musu ₦300,000 ta asusun Opay, zuwa lambar asusun 9026238691 mai suna Abdullahi Lawan Garba, bayan sun harba bindiga don tsoratar da ni,” in ji shi.
Rundunar ta ce kayayyakin da ta kwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da wayoyi shida na zamani, ciki har da iPhone 12 Pro Max, Tecno Camon 40 Pro, Samsung Galaxy A15, Infinix X6531B, da Itel keypad phone, tare da katunan ATM na First Bank, GTBank, da Opay, da kuma agogo, da sauran kayayyaki.
Ya kuma gargadi matafiya da su yi taka-tsantsan musamman a darare, yana mai cewa a yayin da ake ƙaratowa lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, masu aikata laifuka kan ƙara yawaita don cutar da jama’a.
