News
DSS Ta Kori Jami’anta Sama Da 100
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki.
Gwamnan Borno Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Jihar
Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a.
“A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a hukumar DSS, an sallami jami’ai 115. Don haka ana gargaɗin jama’a da su guji yin hulɗa da waɗannan mutanen da aka sallama daga aiki,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na tsaftace hukumar da tabbatar da ingantaccen aiki da gaskiya a tsakanin jami’anta.
