News
Gwamnan Borno Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Jihar
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata, ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye a Jihar.
An rarraba motocin ne da nufin karfafa gwiwar rundunonin tsaron musamman ‘yansanda, da kuma rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar tsaro kamar ‘yan daba da sauran nau’ikan laifuka a cikin babban birnin jihar da ke kewaye.
Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da Yajin Aikin Likitoci A Najeriya
Wannan tallafin yana daya daga cikin dimbin gudummawar da gwamnatin Zulum ke yi tun daga shekarar 2019, wadanda dukkansu an yi su ne don karfafa tsarin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno.
