Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da Yajin Aikin Likitoci A Najeriya

Published

on

Tinubu
Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta sulhunta matsalolin da suka kai ga shiga yajin aikin likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya, tare da tabbatar da komawarsu bakin aiki cikin gaggawa.

Ƙaramin ministan lafiya na Najeriya Dr. Iziaq Salako ne ya bayyana shirin gwamnatin ƙasar na kawo ƙarshen rikicin da ya dabaibaiye fannin kiwon lafiya a sassan ƙasar, bayan ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta bayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani a ƙarshen makon da ya gabata.

Dakarun Sojin Ruwan Ghana Sun Kama ‘Yan Nijeriya 10 Da Suka Ɓuya A Jirgin Ruwa

Salako ya baiwa ‘yan Najeriya haƙuri a madadin babban ministan lafiya Ali Pate da kafatanin ma’aikatan ma’aikatar, bisa yadda harkokin lafiya suka durƙushe, inda likitoci suka ƙauracewa wuraren ayyukansu, a wani yanayi da tarin marasa lafiya ke cikin mawuyacin hali, kuma suka gaza samun kulawa sanadiyyar yajin aikin.

Ƙaramin ministan ya ce shugaba Tinubu ya bayar da umarnin yin duk mai yiwuwa don ganin likitocin sun dawo bakin aiki cikin gaggawa.

Advertisement

Tunda fari dai ƙungiyar likitocin ta shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar domin jan hankalin gwamnatin tarayya don ta biya musu haƙƙoƙinsu.

To sai dai a cewar ƙungiyar ta bai wa gwamnati ƙarin wa’adi na kwanaki 30, amma ta yi burus da kiraye-kirayen su, abinda ya tilasta musu tsunduma yajin aikin a ranar asabar ɗin da ta gabata.

Ko a watan Satumbar nan da ya gabata, ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa ta ce gwamnatin ƙasar ta riƙe wa likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya kuɗaɗensu da ya kai Naira biliyan 38.

 

Advertisement

 

FRI HAUSA

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *