News
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Amfani Da Harshen Hausa A Makarantu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin doka da ke neman amfani da harshen Hausa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare da sakandare a fadin jihar.
Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Musa Ali Kachako, ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar da aka gudanar a yau Talata.
A cewar Kachako, matakin yana da muhimmanci wajen inganta ilimi a matakin farko, domin zai ba ɗalibai damar fahimtar darussa cikin sauƙi tare da rage yawan faduwar jarrabawa da barin makaranta.
Ya ce, kasashe da dama kamar China, Japan da India sun samu ci gaba mai yawa a fannin kimiyya da fasaha bayan amfani da harsunansu na gida wajen koyarwa.
Kachako ya ƙara da cewa dokar za ta taimaka wajen kare al’adun Hausawa da kuma ƙarfafa fahimtar darussan kimiyya da fasaha ga ɗalibai.
Bayan gabatar da kudirin, majalisar ta tura shi zuwa Kwamitin Ilimi domin ƙarin nazari kafin a sake karanta shi a karo na biyu.
