Connect with us

News

‎Kotu Ta Yanke Wa Iyalan Tsohon Shugaban Kasar Gabon Hukuncin Daurin Shekaru 20 A Gidan Kaso ‎

Published

on

Gabon 860x526

Kotun manyan laifuka ta musamman ta yanke wa tsohuwar matar shugaban Gabon da danta hukuncin zaman gidan kaso bayan shari’ar kwanaki biyu a Libreville.

‎An yanke wa Sylvia Bongo da Noureddin Bongo hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda sama da fadi da dukiyar kasa, da halatta kudaden haram, da wasu miyagun laifuka. An kuma umarce su da su biya miliyoyin daloli a matsayin tara saboda laifukan da suka aikata a kan kasar Gabon.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Janye Shirinta Na Amfani Da Harsunan Gida Wurin Koyarwa A Makarantu

‎Sylvia Bongo da Noureddin Bongo Valentin sun yi tasiri a lokacin shekaru 14 na mulkin tsohon shugaban Gabon Ali Bongo a tsakiyar Afirka, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulki a shekarar 2023 bayan ya lashe zaben da aka yi jayayya a kai wanda sojoji da ‘yan adawa suka ce an tabka magudi.

‎Juyin mulkin ya kawo karshen shekaru 56 na daular Bongo a kan mulki.

Advertisement

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending