Connect with us

News

’Yan Fashi Sun Kwashi Kaya A Wani Shago Da Ke Kusa Da Babban Asibitin Makoda

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai hari a karamar hukumar Makoda ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da kaya masu daraja daga wani shago da ke kusa da babban asibitin garin.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa Premier Radio cewa lamarin ya faru ne da daddare a ranar Lahadi, lokacin da wasu ’yan fashi suka shigo garin a kan babura dauke da bindigogi, inda suka fara harbi a sama don tsoratar da jama’a.

Advertisement

‎Kotu Ta Yanke Wa Iyalan Tsohon Shugaban Kasar Gabon Hukuncin Daurin Shekaru 20 A Gidan Kaso ‎

“Sun zo da misalin karfe goma na dare, suka yi ta harbi a sama. Mutane sun watse domin tsira da rayukansu. Daga nan suka kwashi kaya daga babban shago da wasu kananan shaguna kafin su tsere,” in ji wani ganau.

Rahotanni sun ce babu wanda ya mutu ko ya ji rauni a harin, sai dai an yi asarar dukiya mai yawa daga shagunan da aka farma.

Advertisement

Al’ummar yankin sun bukaci hukumomin tsaro da su dauki mataki don tabbatar da tsaro a Makoda da yankunan da ke kewaye, domin hana maimaituwar irin wannan farmaki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending