Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Matasa Daurin Shekaru Uku Saboda Cire Password Din Wayar Sata A Kano 

Published

on

images (7)

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba uku da ke Sakatariyar Audu Bako, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan, ta yanke wa wasu matasa hukuncin daurin shekaru uku–uku ko biyan tarar naira dubu dari biyu, bayan ta same su da laifin cire password din wata waya da aka sace tare da ɗaukar kuɗi daga cikinta.

Rahoton Arewa Updates ya bayyana cewa, an gurfanar da Abdulkadir Aminu, Abdulkadir Abdullahi, Saifullahi Salisu, Jibril Yunusa, da Nasir Yunusa a gaban kotun bisa zargin haɗin baki wajen aikata fashi da makami da kuma jikkata wata mata mai suna Ramlat Usman, wadda suka yi wa fashin waya.

Advertisement

Bayan gabatar da hujjoji daga lauyoyin gwamnati, kotun ta tabbatar da laifin da aka tuhuma Abdulkadir Abdullahi da Nasir Yunusa da shi, inda ta same su da laifin taimaka wa masu fashi da makami.

Mai Shari’a Faruk Lawan ya yanke musu hukuncin daurin shekaru uku–uku a gidan yari, ko kuma su biya tarar naira dubu dari biyu kowannensu a madadin zaman gidan yari.

Advertisement

Kotun ta kuma sanya ranar 16 ga Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku da ke fuskantar tuhumar fashi da makami kai tsaye

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending