Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Janye Shirinta Na Amfani Da Harsunan Gida Wurin Koyarwa A Makarantu

Published

on

FB IMG 1762488671790

Gwamnatin Tarayya ta umurci malamai a fadin kasar da su ci gaba da amfani da harshen Turanci a matsayin harshen koyarwa a makarantu, lamarin da ke nuna cewa shirin da aka yi na koyarwa da harsunan gida bai samu karɓuwa ba.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron kasa da kasa kan Harshen Ilimi na 2025, wanda Majalisar Burtaniya ta shirya a birnin Abuja.

Advertisement

Gwamnatin Tarraya Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

A cewar Ministan, wannan matakin na gwamnati ya biyo bayan bukatar da ta taso ta inganta koyo da kuma tabbatar da daidaito a tsarin koyarwa a duk fadin kasar.

Taron ya tattaro kwararru daga sassa daban-daban ciki har da masana, masu tsara manufofi, masana ilimi, masu bincike da abokan hulɗa daga Afirka, Kudancin Asiya da Birtaniya domin tattauna hanyoyin inganta koyo ta amfani da harshe.

Advertisement

Dr. Alausa ya jaddada cewa duk da muhimmancin kiyaye harsunan asali wajen tabbatar da al’adunmu, Turanci ne ya kamata ya ci gaba da zama harshen koyarwa tun daga matakin firamare har zuwa makarantu na gaba da sakandare.

Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta fahimtar dalibai da kuma daidaita gogayyar ilimi tsakanin ɗaliban Najeriya da takwarorinsu na sauran ƙasashe.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending