News
Yan sanda sun kama kunshi 66 na tabar wiwi a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke ƙunshi 66 na tabar wiwi a garin Deba, bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri.
Lamarin ya faru ne da misalin 9:30 na dare, ranar 16 ga Nuwamba, 2025, inda aka hango mota mara lamba, Toyota Corolla, a hanyar Kuri–Deba tana ɗauke da kaya.
Da jami’an suka isa wurin, sun tarar da mutum uku na ƙoƙarin lodawa wani mutum kaya a kan babur. Sun tsere bayan ganin ’yan sanda.
Bincike ya kai ga gano buhuna uku masu ɗauke da ƙunshe-ƙunshe 66 na tabar wiwi. An kwashe kayan zuwa ofishin ’yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike domin kamo waɗanda suka gudu.
Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Bello Yahaya, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaki da masu safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
