News
Kotu Ta Yanke Wa Farfesa Hukuncin Shekaru 5 A Gidan Yari
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Farfesa Cyril Ndifon, tsohon Shugaban Sashen Shari’a na Jami’ar Calabar (UNICAL), hukuncin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, kan tuhumar cin zarafin dalibai mata.
Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa hukumar ICPC ta tabbatar da tuhumar da take yi wa Ndifon a kan laifuka biyu na farko, inda ta gabatar da hujjoji “sosai fiye da tsammani.” Saboda haka kotu ta yanke masa shekaru biyu a laifi na farko, sannan shekaru biyar a na biyu, waɗanda za su gudana tare.
Kotun Bangladesh Ta Yanke Wa Tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina Hukuncin Kisa
A cikin bayanan ICPC, Ndifon — a lokacin da yake Dean — ya tilasta wa wata dalibar Diploma, mai suna TKJ, ta tura masa hotunan batsa ta WhatsApp, tare da sake neman ta yi masa “blow job” a matsayin sharadin samun gurbin karatu a sashen Shari’a na jami’ar.
Hukumar ta zargi Farfesan da cin zarafin dalibai mata da dama, yana amfani da matsayinsa na shugabanci domin samun abinda yake so.
Daga ƙarshe kotu ta tabbatar da hukuncin shekarun da ta yanke wa Ndifon, a matsayin darasi ga duk masu rike da mukaman gwamnati da ke amfani da ofishinsu wajen cin zarafin mata ko lalata shari’a.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News14 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
