News
An Tura Wani Matashi Gidan Kurkuku Bayan Ya Yaga Hotan Shugaban Kasa
Wani matashi mai suna Mouhamadou Bachir Syll a Senegal ya shiga hannun hukuma bayan da ya yaga hoton shugaban kasa, Bassirou Diomaye Faye, lamarin da ya janyo cece-kuce a kasar.
Ofishin ‘yan sanda na tsakiyar birnin Saint-Louis ya kammala bincike kan lamarin, inda aka gurfanar da Syll gaban kotu a safiyar Juma’a bisa zargin cin fuska ga shugaban kasa da kuma zagon kasa ga Shugaban a bainar jama’a.
Bayan gabatar da rahoton farko, babban jami’in shari’a, Baye Thiam, ya bukaci a bude cikakken binciken shari’a, inda ya nemi a fitar da takardar cafke matashin.
Daga nan ne alkalin Babbar Kotun Saint-Louis ya tuhumi matashin, sannan aka tura shi Gidan kurkuku. Ana sa ran zai yi daren farko a gidan yari yayin da shari’a ke ci gaba.
A cikin ‘yan kwanakin baya, wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna matashin yana fasa hoton shugaban kasa a matsayin “dan kasa mai kishin ƙasa”, inda kuma ya yi wasu maganganu na rashin kunya da cin fuska kan shugaban. Wannan bidiyo ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin al’umma.
