Connect with us

News

Kaso 90 Na Makarantun Dake Koyar Da Harkar Jinya A Najeriya Basu Da Shaidar Izini Daga Gwamnati

Published

on

Nurses

Shugaban Hukumar Rajistar Ma’aikatan Kiwon Lafiya ta Najeriya (HPR), Dr. Alhaji Bashir Idris, ya bayyana cewa mafi yawan makarantun da ke koyar da ilimin jinya a fadin ƙasar — kimanin kashi 90 cikin 100 — ba sa da sahalewar aiki daga gwamnati.

Dr. Idris ya bayyana hakan ne a cikin shirin Barka da Warhaka na Freedom Radio Kaduna, yayin da yake bayyana damuwar hukumarsa kan yadda ake ta yawaitar kafa makarantu marasa rajista da kuma barazanar da hakan ke haifarwa ga tsarin kiwon lafiya.

Advertisement

Kaso 90 Na Makarantun Dake Koyar Da Harkar Jinya A Najeriya Basu Da Shaidar Izini Daga Gwamnati

A cewarsa, hukumarsu ba ta da cikakken rajista ko bayanan sahihanci kan yawancin wadannan makarantu, lamarin da ya ce na janyo cunkoson dalibai da kuma fitar da ƙwararrun da ba su da ingantacciyar horo, wanda ke iya jefa rayuwar marasa lafiya cikin haɗari.

Ya ce hukumar tana aiki tare da hukumomin tsaro da sauran bangarorin gwamnati domin dakile yaduwar irin wadannan cibiyoyi da ba su bin ka’ida.

Advertisement

Dr. Idris ya kuma ja hankalin iyaye da matasa masu neman shiga makarantar jinya da su rika tantance sahihancin kowace makaranta kafin su yi rajista, domin kaucewa asarar lokaci da kuɗi, da kuma kare lafiyar al’umma.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending