Connect with us

News

Amurka Na Fuskantar Suka Kan Kiran Soke Shari’ar Musulunci A Arewacin Najeriya

Published

on

Kungiyoyin addini da na farar hula daga Arewacin ƙasar na ci gaba da maida martani kan wani zama da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi, inda wasu suka buƙaci a matsa wa Najeriya lamba domin ta soke Shari’ar Musulunci da hukumomin Hisbah a jihohin Arewa.

Masu wannan buƙata sun yi ikirarin cewa tsarin shari’ar Musulunci da ayyukan Hisbah na taka rawa wajen cin zarafin Kiristoci a yankin.

Advertisement

Kaso 90 Na Makarantun Dake Koyar Da Harkar Jinya A Najeriya Basu Da Shaidar Izini Daga Gwamnati

Majalisar Koli ta Tabbatar da Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta yi watsi da kiran. Babban sakatarenta, Dakta Nafi’u Baba-Ahmed, ya shaida wa BBC cewa

“Shari’a ruhin Musulmi ce. Maganar cewa wai a kauda ta wani mafarki ne. Duk wanda ke tunanin hakan ya sani Musulmi ba za su bari ba.”

Advertisement

Ya ce maganar raba “shari’ar ’yan siyasa da shari’ar ba ’yan siyasa ba” wani salo ne da “makiyan Musulunci ke amfani da shi.”

A cewarsa, ko wace irin matsin lamba da kasashen waje za a yi, “ba za ta sauya matsayin Musulmi ba.”

Advertisement

Dangane da kiran da ake yi na rushe hukumomin Hisbah, Dakta Nafi’u ya ce:

“Idan aka taba Hisbah, shari’a aka taba. Wannan ba abin wasa ba ne. Idan hakan ta kawo rikicewa, masu tayar da batun su sani akwai abin da zai biyo baya.”

Advertisement

Ya kuma ce za su nuna adawa a matakin siyasa idan gwamnati ta rungumi irin wannan matsin lamba, musamman a zaben 2027.

Gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta maida martani ta bakin shuganta, Komred Jamilu Aliyu Charanchi, inda ya ce akwai ƙoƙarin da ake yi na “dora matsalolin Najeriya a kan Shari’ar Musulunci,” duk da cewa, a cewarsa:

Advertisement

“Ba a taɓa ganin wanda ba Musulmi ba da aka gurfanar a kotun shari’a aka hukunta shi ba.”

Ya ce akwai “ƙungiyoyi da kasashen waje” da ke da kiyayya ga Arewa da Musulunci, waɗanda ke neman amfani da irin waɗannan muhawara domin raunana yankin.

Advertisement

“A zabe mai zuwa dole ’yan Arewa su zabi shugabannin da za su kare mutuncinsu,” in ji shi.

Tun kusan shekara 20 da su ka gabata ne jihohi da dama na Arewa suka fara aiwatar da Shari’ar Musulunci domin inganta tarbiyya da al’adu, da magance matsalolin zamantakewar al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending