Connect with us

News

Amurka Ta Tsaurara Sharuɗɗan Ba Da Biza Ga ‘Yan Najeriya

Published

on

us visa

Amurka ta sanar da wasu jerin tsauraran sauye-sauye a tsarin bayar da takardar izinin shiga ƙasarta ga masu zuwan wucin-gadi daga Najeriya, inda a yanzu ta zaftare wa’adin bizar da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ƴan Najeriya.

Matakin ya fara aiki ne tun daga ranar 8 ga watan Yuli, kuma ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce kusan dukkanin bizar da take ba wa ƴan Najeriya ta masu zuwan wucin-gadi ce, wato ba masu zuwan zaman dindindin ba da kuma bizar da ba ta diflomasivya ba, da za ta ba ƴan Najeriya za ta kasance ne ta shiga ɗaya kacal .

Advertisement

Ƴan Ƙabilar Igbo Ne Ke Aikata Laifuka A Kudu, Ba Fulani Makiyaya Ba – Gwamna Soludo

Ta kuma ce ta iya wa’adin wata uku ne – saɓanin da yadda take bayar da biza ɗaya da wa’adin shekara ɗaya ko ma fin haka kuma ɗan Najeriya ya shiga Amukar sau da dama.

BBC HAUSA ta ruwaito cewa Sanarwar ta ce wannan na daga cikin matakin da Amurka ta ɗauka na sake tsarin alaƙarta ta cuɗan-ni-in-cuɗe-ka da ƙasashen duniya.

Advertisement

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce manufofi da tsare-tsaren bayar da biza na daga abubuwan da ake iya sauvawa a ko da yaushe – wanda kuma za a iya sauyawa ɗin dogaro da yanayin alaƙar diflomasiya da tsaro da ka’idoji ko yanayin shige da fice.

A sanarwar gwamnatin Amuka ta ce tana aiki ƙut da ƙut da hukumomin Najeriya domin tabbatar da ganin Najeriya ta daidaita al’amuranta kamar yadda ya dace da tsarin manyan ƙasashen duniya – ta fannin :

Advertisement

1 Bayar da takardun tafiye-tafiye masu tsaro

2 Da hana wuce wa’adin da aka ɗiba wa mutum a biza

Advertisement

3 Da kuma musayar bayanan da suka shafi tsaro ko wani mugun laifi saboda dalilai na kare lafiyar jama’a.

Ƴan Najeriya masu yawon buɗe idanu da dalibai da ƴan kasuwa masu tafiye tafiye na daga cikin waɗanda wannan sauyi mai tsauri na bayar da bizar Amurkar zai shafa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending