News
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Ƙara Kuɗin Wutar Lantarki
Gwamnatin Tarayya ta ce tana duba yiwuwar ƙara kuɗin wutar lantarki a ƙasar nan domin rage giɓin bashin da masana’antar lantarki ke ciki, wanda ya kai naira tiriliyan huɗu.
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja, inda ya ce dole ne gwamnati ta daina ɗaukar nauyin tallafin da take ba wa kamfanonin lantarki, domin hakan yana hana masana’antar inganta ayyukanta.
A cewar Adelabu, ƙarin kuɗin lantarki shi ne kadai mafita wajen ceto masana’antar daga durƙushewa da kuma tabbatar da cewa jama’a na samun wutar da ta dace.
Ya ce, “Gwamnati ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin wuta ba. Matakin da muke ɗauka yana nufin ceton masana’antar ne da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa.”
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa a cikin watanni shida na farkon shekarar 2025 kadai, gwamnati ta kashe naira tiriliyan ɗaya da miliyan ɗaya wajen biyan tallafin lantarki, wanda hakan ke ƙara nauyi a aljihunta.
Ministan ya ce akwai bukatar a cire tallafin domin a tabbatar da dorewar harkokin masana’antar lantarki.
Duk da cewa gwamnati ta riga ta ƙara wa kwastomomin da ke tsarin Band A kuɗin wuta, har yanzu mutane da dama na ƙorafi cewa wutar ba ta isa ba.
Amma Minista Adelabu ya ce matakin zai amfani ƙasa baki ɗaya, domin yana ɗaya daga cikin hanyoyin farfaɗo da ɓangaren wutar lantarki da kuma rage dogaro da gwamnati.
Ya ce, “Idan ba mu ɗauki matakin yanzu ba, to masana’antar na iya durƙushewa gaba ɗaya.”
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
