News
NEC Ta Amince Da Naira Biliyan 100, Don Gyara Cibiyoyin Horas Da ‘Yansanda
Majalisar Tattalin Arziki ta Nijeriya (NEC) ta amince da naira biliyan 100, domin gyaran cibiyoyin horas da ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin ƙasar.
An ɗauki wannan matakin ne a taron majalisar na 154, wanda aka gudanar ta intanet a ranar Laraba, bayan gabatar da rahoton kwamitin wucin-gadi da aka kafa domin tantance halin da cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro ke ciki.
Amurka Na Fuskantar Suka Kan Kiran Soke Shari’ar Musulunci A Arewacin Najeriya
Majalisar ta kuma amince da N2.6 biliyan domin biyan kudin masu ba da shawara kan aikin.
Sai dai duka waɗannan kuɗaɗen da aka amince sai sun jira amincewar shugaban ƙasa kafin a fitar da su.
Tun a taron NEC na 152 a watan Oktoba Shugaba Tinubu ya bayar da shawarar fara gagarumin gyara da sabunta cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro a fadin ƙasa.
Shugaban kwamitin kuma Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana cewa yawancin cibiyoyin suna cikin mawuyacin hali, suna kuma bukatar a gyara su a cikin gaggawa.
Bayan gabatar da rahotonsa, Shugaban Majalisar Tattalin Arikin Ƙasa kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na magance matsalar, tare da jaddada buƙatar ganin sauye-sauye suna haifar da sakamako kai tsaye ga ‘yan kasa.
Shettima ya yi kira ga gwamnonin jihohi su tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin jihohinsu suna haifar da ingantuwar rayuwar jama’a, yana mai jaddada cewa ana auna sakamakon da gwamnati ta samar ba wai alƙawura ba.
