Connect with us

News

‎Amurka Ba Ta Da Hurumin Zabar Mana Yadda Za Mu Rayu Ko Shugabanci Ko Salon Addini A Najeriya  ‎ ‎ ‎—Bashir Ahmad

Published

on

images (8)
‎Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta Bashir Ahmad

‎Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya bayyana cewa Amurka ba ta da ikon tsoma baki akan yadda za mu rayu ko shugabanci ko salon addinin Najeriya, yana mai cewa kasar “cikakkiyar ƙasa ce mai kundin tsarin mulki.”

‎Ahmad ya fadi haka ne bayan wani rahoto da ya nuna cewa wasu kwararru a Amurka sun nemi ‘yan majalisar dokokin kasar su matsa wa Najeriya domin soke shari’ar Musulunci da ruguza hukumomin Hisbah a jihohin Arewa.

Advertisement

Hukumar Kashe Gobara Tayi Gargaɗi Kan Amfani Da Wuta A Lokacin Sanyi A Kano

‎Wadannan kwararru sun yi zargin cewa tsarin shari’ar Musulunci da ayyukan Hisbah na taimakawa wajen nuna wariya ga bangaren Kiristoci a Najeriya.

‎A zaman da aka yi a majalisar wakilai a Amurka, kwararre a cibiyar Council on Foreign Relations, Dr. Ebenezer Obadare, ya ce kungiyoyin Boko Haram, ISWAP da wasu kungiyoyin makiyaya masu tsattsauran ra’ayi na amfani da tsarin shari’a da hukumomin Hisbah wajen yada akidunsu da kuma aiwatar da ayyukan tilastawa.

Advertisement

‎Da yake mayar da martani a shafinsa na X, Bashir Ahmad ya ce batun ya zama “tsoma baki kai tsaye cikin harkokin cikin gida na Najeriya,” duk da cewa bai so ya ci gaba da tattaunawa a kai ba.

‎Ya kara da cewa Amurka ba ta da hurumin gaya wa Najeriya yadda ya kamata ta rayu ko ta gudanar da mulkinta da addininta.

Advertisement

‎A rubutunsa, Ahmad ya ce:

‎“Amurka ba ta da hurumin zabar mana yadda za mu rayu ko shugabanci ko salon addini,Najeriya cikakkiyar kasa ce mai kundin tsarin mulki da kuma al’adunta.”

Advertisement

TRIBUNE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending