Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Haramtawa Ɗaliban SS2 Zana Jarrabawar Kammala Sakandire 

Published

on

FB IMG 1762488671790

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da haramta karɓa ko sauya ɗalibai zuwa aji na Senior Secondary School Three (SS3) a dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar, a wani mataki na dakile yawaitar maguɗin jarrabawa.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙaruwa da ake samu na maguɗin jarrabawa, musamman ta hanyar amfani da abin da aka fi sani da “special centres”, wanda ke tauye sahihanci da mutuncin jarrabawar ƙasa.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Kafa Runduna Ta Musamman Da Za Ta Ke Tsaron Tashoshin Mota ‎

A wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Lahadi, 14 ga Disamba, 2025, an bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga shekarar karatu ta 2026/2027.

Sanarwar ta ce daga lokacin, za a takaita karɓa da sauya ɗalibai zuwa SS1 da SS2 kawai, yayin da duk wani motsi ko karɓar ɗalibi zuwa SS3 zai kasance haramun.

Advertisement

Ma’aikatar ta ce manufar matakin ita ce hana motsa ɗalibai a ƙarshen karatunsu domin neman fa’ida a jarrabawa, tare da ƙarfafa sa ido kan koyarwa da tabbatar da adalci a tsarin tantance ilimi.

Gwamnatin Tarayya ta kuma gargadi masu makarantu da hukumomin kula da ilimi da su bi umarnin, tana mai cewa duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukunci bisa ƙa’idojin ilimi da dokokin ƙasa.

Advertisement

 

KAKAKI24

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending