News
Wasu Bata-gari Sun Hallaka Wata Mata Mai Juna Biyu Da Ɗanta A Kano
Mazauna unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke cikin birnin Kano sun shiga firgici, bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe wata mace mai juna biyu tare da ƙona ta ita da ɗanta mai watanni 18.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar, lokacin da mijin matar ya dawo gida daga wurin aiki da misalin ƙarfe 8 na dare, inda ya tarar da ƙofar gidansa a kulle daga waje.
Gwamnatin Tarayya Ta Haramtawa Ɗaliban SS2 Zana Jarrabawar Kammala Sakandire
An ce bayan ya balle ƙofar, sai ya shiga ya tarar da gawar matarsa da ɗansu a kwance, bayan an kai musu hari tare da ƙona su, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin alhini da firgici.
Wani jagoran al’umma a yankin, Ahmad Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai nuna damuwa kan ƙarancin tsaro da yankin ke fuskanta.
A cewarsa, mazauna unguwar sun gina ofishin ‘yansanda domin ƙarfafa tsaro, amma har yanzu ba a tura jami’an tsaro domin kula da ofishin ba.
Ya yi kira ga Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kano, Ibrahim Bakori, da ya gaggauta ɗaukar mataki ta hanyar tura jami’an tsaro zuwa yankin domin hana sake aukuwar irin wannan hari.
Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yansanda a Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike, tare da tabbatar da cewa za a kamo waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban kotu.
