News
Gwamnatin Tarayya Ta Wajabta Gwajin Ta’ammali Da Muggan Ƙwayoyi Ga Masu Neman Aikin Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati su sanya gwajin miyagun ƙwayoyi a matsayin sharadi na wajibi kafin ɗaukar sabbin ma’aikata aiki.
Umarnin ya fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, inda aka bukaci hukumomin gwamnati su yi aiki tare da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin gudanar da gwaje-gwajen bisa ƙa’idoji.
Gwamnatin ta ce matakin na da nufin rage yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa, tare da kare lafiyar jama’a, inganta nagartar aiki, bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa tsaron ƙasa.
Wannan mataki na cikin jerin manufofin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na shekarar 2025 da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa.
A baya-bayan nan, wasu hukumomi kamar Hukumar Kwastam ta Najeriya, da kuma wasu jami’o’i, sun fara aiwatar da gwajin miyagun ƙwayoyi ga sabbin ma’aikata da ɗalibai, a wani yunƙuri na ƙasa baki ɗaya na magance matsalar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
