News
An Sace Mutane 28 A Hanyarsu Ta Zuwa Maulidi A Filato
’Yan bindiga sun sace mutane 28 da ke hanyarsu ta zuwa taron Maulidi a Zak da ke a Jihar Filato
Maharan su yi garkuwa da matafiyan ne a daren Lahadi a kauyen Zak, da ke gundumar Bashar, ta Ƙaramar Hukumar Wase ta jihar.
An Cafke ‘Yan Mata Biyu Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Kwayoyi Cikin Gidan Yari A Kano
Wani jagoran matasa a Wase, Shafi’i Sambo, ya ya shaida wa wakilinmu ya wayar tarho cewa wadanda aka sace sun haɗa da maza, mata da yara.
Shafi’i Sambo ya ce, ’ya’ya sarakuna biyu da wani jagoran addini da ke jagorantar tafiyar suna cikin wadanda aka sace.
Ya ce, “Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa Sabon Layi domin taron. Lokacin da ’yan bindigar suka tare motar da ke ɗauke da matafiyan a wajen kauyen, suka tafi da dukkan matafiyan ciki har da yara, suka bar motar a wurin.
“Da safiyar Litinin ne wasu matafiya da ke bi ta hanyar suka ga motar, wacce ta mallaki shugaban kauyen Zak, a ajiye a hanya.
“A yayin bincike ne al’umma suka gano cewa motar da ke dauke da matafiyan ce aka ajiye,” in ji Shafi’i.
Wani mazaunin garin Bashar, Ibrahim Musa, ya ce har yanzu ba a san inda aka kai waɗanda aka sace ba.
A cewarsa, an sace mutanen ne a hanyarsu daga kauyen Zak zuwa yankin Sabon Layi domin halartar taron Maulidi da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi.
Shafi’i Sambo ya ce duk ƙoƙarin gano inda aka kai mutanen bai yi nasara ba, yana mai ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro game da lamarin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Alabo Alfred, ya ce suna binciken rahoton lamarin a lokacin da aka tuntube shi.
AMINIYA ta ruwaito cewa garkuwa da mutane, ta’addanci da satar shanu sun yi ƙamari a yankin Wase baki ɗaya, inda mazauna ke kira ga jami’an tsaro da su kawar da miyagun da ke addabar yankin
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News2 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
