Connect with us

News

Jami’an Yansanda Sun Cafke Fitaccen Dan Fashi Da Makami Abba Fiya A Kano 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wani fitaccen wanda ake zargi da fashi da makami mai suna Abba Aliyu, wanda aka fi sani da Abba Fiya, mai shekaru 26, a unguwar Dala da ke Kano.

Mai magana da yawun Ƴansandan Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, an cafke wanda ake zargin ne a ranar 21 ga Disamba yayin da jami’an sashin Anti-Daba ke amsa kiran gaggawa kan wani lamari na fashi da makami a yankin unguwar Hausawa, bisa umarnin Kwamishinan Ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Wajabta Gwajin Ta’ammali Da Muggan Ƙwayoyi Ga Masu Neman Aikin Gwamnati

Rundunar ta ce a lokacin kama shi, an kwato wuka mai kaifi daga hannunsa, kuma ya amsa laifin aikata fashi da makami da kuma faɗace-faɗacen daba a yankunan Gobirawa Gangare, Dala, da Tudun Fulani Mayanka a Kano.

Bincike ya kuma nuna cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya na da hannu a wasu hare-haren fashi da suka yi sanadiyyar rasa rayuka, jikkata mutane da satar dukiyoyi a jihohin Kano, Rivers da Lagos.

Advertisement

Rundunar ta bayyana cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Kwamishinan Ƴansandan jihar ya yaba wa jami’an da suka kai ga wannan nasara, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ake zargi ta lambobin gaggawa na rundunar

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending