News
Ofishin Jakadancin Amurka Ya Sanar Da Dakatar Da Bayar Da ‘Visa’ Ga ‘Yan Najeriya
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya sanar da dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya, matakin da zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
Sanarwar, wadda ofishin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, ta ce matakin na cikin umarnin Shugaban Ƙasar Amurka mai lamba 10998, wanda aka ce an ɗauke shi ne domin ƙarfafa tsaron ƙasar.
Jami’an Yansanda Sun Cafke Fitaccen Dan Fashi Da Makami Abba Fiya A Kano
A cewar ofishin, dakatarwar ta shafi nau’o’in ‘visa’ da suka haɗa da visa’ yawon buɗe ido da kasuwanci (B-1/B-2), visa’ karatu da musayar ɗalibai (F, M, J), da kuma visa’ zama na dindindin a Amurka.
Nijeriya na daga cikin ƙasashe 19 da wannan mataki ya shafa. Sauran ƙasashen sun haɗa da Angola, Benin, Burundi, Côte d’Ivoire, Cuba, Gambia, Malawi, Mauritania, Senegal, Tanzania, Togo, Venezuela, Zambia da Zimbabwe, da wasu ƙasashe.
Sai dai ofishin ya ce akwai keɓantattun rukuni da wannan dakatar war ba ta all shafa da dakatarwar ba.
Waɗannan sun haɗa da masu riƙe da fasfo biyu, wasu rukunin ’yan ƙananan ƙabila ko addinai da ke fuskantar tsanantawa, ma’aikatan gwamnatin Amurka masu visa’ Special Immigrant Visa (SIV), da kuma masu izinin zama na dindindin a Amurka.
Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa duk wanda ke da visa’ mai inganci kafin 1 ga Janairu, 2026, ba zai shiga cikin wannan doka ba, tare da tabbatar da cewa ba za a soke wata biza da aka bayar kafin wannan rana ba.
