News
Trump Ya Ƙara Nijeriya Da Wasu Ƙasashe 12 Cikin Jerin Masu Biyan Kimanin Naira Miliyan 22 Don Neman Bizar Amurka
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump ta faɗaɗa jerin ƙasashen da ake buƙatar ’yan ƙasarsu su biya kuɗin ajiya kafin samun bizar shiga ƙasar, wanda adadinsa ya kai $15,000. Wannan mataki zai fara aiki ne daga 21 ga Janairu, 2026, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar.
Sabon tsarin ya kusan ninka yawan ƙasashen da abin ya shafa, inda aka ƙara ƙasashe 25, ciki har da Nijeriya, zuwa jerin da yanzu ya kai ƙasashe 38 mafi yawan su daga Afirka, Latin Amurka, da Asiya. Sabbin ƙasashen da aka karaa sun haɗa da Algeria, Angola, Benin, Burundi, Cabo Verde, Djibouti, Gabon, Côte d’Ivoire, Senegal, Togo, Uganda, da Zimbabwe.
KALVEJ Ƙungiya Ce Mai Zaman Kanta Ta, Ba Ta Ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai — Waiya
Gwamnatin Trump ta bayyana cewa wannan mataki na nufin rage yawan masu wuce lokacin bizar su a Amurka. Duk da haka, an tabbatar cewa biyan kuɗin ajiyar ba yana nufin an samu biza ba ne, kuma za a mayar da kuɗin idan mai nema bai samu bizar ba ko kuma idan mai nema ya cika duk sharuddan da ake buƙata.
