Connect with us

News

‎EFCC Ta Saka Naira Bliyan 3.2 Don Tsaftace Ofisoshinta Da Kayan Makwalashe A Kasafin Kuɗin 2026

Published

on

Spread the love

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC  ta shirya kashe N3.2 biliyan domin tsaftace ofisoshinta da kuma abinci da kayan makwalashe a kasafin kuɗin 2026.

‎A cewar jaridar Daily Trust, wannan bayani na kunshe ne a sashen kudaden da fadar shugaban kasa za ta kashe na kundin kasafin da Shugaban Tinubu ya gabatar wa majalisar dokoki a ranar 19 ga Disamba, 2025.

‎Takardun kasafin kuɗin da aka samu daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya sun nuna cewa EFCC ta ware Naira miliyan 278.6 don tsaftace ofisoshinta, sannan Naira miliyan 722 don abinci da kayan makwalashe.

Advertisement

‎Hukumar ta kuma tanadi Naira biliyan 1.02 don sayen man fetur a motocinta, da Naira biliyan 1.2 don samar da mai ga injinan wutar lantarki. Hakan ya sa jimillar kuɗin da aka ware kan waɗannan fannoni ta haura Naira biliyan 3.2.

‎Bugu da ƙari, kasafin ya nuna cewa an tanadi Naira miliyan 170.5 don magunguna da kayan jinya, Naira miliyan 376.5 don gyaran motoci, da Naira miliyan 46 don gyaran kayan ofis

‎An kuma ware Naira biliyan 1.5 don gyaran gine-ginen ofisoshi da gidajen ma’aikata, tare da Naira miliyan 159.8 don gyaran kayan ofis da na’urorin sadarwa

Advertisement

‎Adadin kudin ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin ya yi yawa a irin halin matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu. Wasu kuma na bayyana cewa irin waɗannan kudade na daga cikin abin da ake dora wa hukumomin tarayya domin gudanar da aikinsu na yau da kullum.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *