News
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Rigakafin Shanu Miliyan 1.5 Don Dakile Cutar CBPP
Gwamnatin Jihar Kano ta fara wani shirin rigakafi a fadin jihar domin kare kimanin shanu miliyan 1.5 daga cutar da ke yiwa huhu da hantar dabbobi, musamman na shanu, illa , da ake kira CBPP da ke haddasa asarar dabbobi da barazana ga wadatar abinci.
Sanarwar da Ma’aikatar Kula kiwon Dabbobi ta Jihar Kano ta fitar ta ce an fara aiwatar da shirin na shekarar 2026 a karamar hukumar Bunkure, kuma za a fadada shi zuwa dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Da Dumi-Dumi :An ga watan Ramadan a Saudiyya
Jami’an kiwon dabbobi sun bayyana cewa cutar CBPP na haddasa raguwar kiba ga shanu, karancin samar da madara, lalacewar ingancin nama, har ma da mutuwar dabbobi. Sun ce cutar na jawo asara ga makiyaya, tare da iya shafar wadatar nama idan ba a dauki mataki cikin lokaci ba.
Kwamishinan ma’aikatar, ya bukaci makiyaya da masu kiwon dabbobi su ba da hadin kai ta hanyar gabatar da shanunsu domin yi musu allurar rigakafi, domin hadin kan al’umma na da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar cututtuka.
Haka kuma, an bayyana cewa kafa ma’aikatar kula da Kiwon dabbobi da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi, wani mataki ne na karfafa lafiyar dabbobi da bunkasa harkar kiwo a jihar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
