Connect with us

News

Da Dumi-Dumi :An ga watan Ramadan a Saudiyya

Published

on

FB IMG 1771340679829

Hukumomin kasar Saudiyya sun umurci a fara azumi daga gobe Labaraba, 18 ga watan Fabareru na 2026

A yau Talata ne rahotanni ke cewa an ga jinjirin watan azumin Ramadan a sassa daban daban na kasar Saudiyya.

Advertisement

Jami’an ’Yan Sanda Sun Ceto Mutumin Da Zargi Mahaifinsa Ya Daure Shi Da Sarka Tsawon Shekaru 17

Hukumomi sun umurci a fara azumi daga gobe Laraba.

Advertisement

Shafin Haramain Sharifain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce, “an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447 wato shekarar 2026 a Saudiyya.

Tunda farko babbar kotun Ƙolin Saudiyya ce ta yi kira ga dukkan Musulmi a faɗin ƙasar da su fita domin neman jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 Sha’aban 1447AH, daidai da 17 ga Fabrairu, 2026 bisa kalandar Umm Al-Qura.

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa za’a fara Sallar Asham a kasar musamman masallacin Ka’aba da na Madina wato Masallacin Annabi Muhammad SAW.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending