Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Ceto Mutumin Da Mahaifinsa Ya Daure Shi Da Sarka Tsawon Shekaru 17

Published

on

1771333004236

Rundunar Ƴan Sanda reshen jihar Bauchi ta sanar da ceto wani mutum mai matsakaicin shekaru, Muhammad Lawan wanda aka fi sani da Babangida, bayan da ake zargin mahaifinsa ya tsare shi a cikin gida tare da daure shi da sarka tsawon shekaru goma sha bakwai.

Lamarin ya fito fili ne bayan wani dan kishin kasa ya sanar da jami’an tsaro cewa mutumin na tsare a gidan mahaifinsa ba tare da kulawa ba.

Advertisement

Tsarin Siyasar Kano : Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura

A cewar rundunar, jami’ai karkashin jagorancin DPO na B Division tare da kakakin ’yan sanda sun kai samame kauyen Shadawanka, inda suka samu mutumin cikin mawuyacin hali, yana fama da tsananin yunwa da rauni.

Advertisement

Jami’an tsaron sun kama mahaifin mutumin, Mohammed Lawan, wanda ake zargi da tsare shi, kuma yanzu yana hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

A halin yanzu, an garzaya da wanda aka ceto asibiti domin samun kulawar gaggawa, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan dalilan da suka haddasa lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement

ALBARKA RADIO

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending