Connect with us

News

Yadda Tankar Mai Ɗauke Da Lita 33,000 Ta Afka Cikin Shago Ana Taka Da Cinikayya ‎ ‎

Published

on

IMG 20260221 WA0003

Wata tankar mai ɗauke da lita 33,000 na man fetur ta afkawa wani shagon gefen hanya, inda mutum ɗaya ya rasa ransa, hudu kuma suka jikkata.

‎Lamarin ya faru ne a Ekoro Junction, hanyar Abule-Egba da ke Legas, lokacin da tankar ta bugi wata mota ƙirar Toyota sakamakon matsalar birki, kafin daga bisani ta afka wa shagon da ke bakin hanya.

Advertisement

An Samu Ƙarancin Fitowar Masu Kaɗa Ƙuri’a A Zaɓen Cike Gurbi A Kano

‎Shaidu sun ce tamkar ta ƙwace wa direban, inda ya buga Toyotar, sannan tasirin bugun ya tura su cikin shagon da ake tsaka da cinikayya.

Advertisement

‎A sakamakon hatsarin, mutum ɗaya ya mutu nan take, yayin da aka garzaya da sauran da suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa. Har yanzu ba a bayyana sunan wanda ya rasu ba, saboda jiran sanar da ‘yan uwansa.

‎Babban Daraktan Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Legas (LASTMA), Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 7:30 na yamma.

Advertisement

‎Ya ce tankar MACK mai lambar EKY 900 XY ta afkawa motar Toyota Corolla mai lambar AAA 823 AY bayan ta samu matsalar birki.

‎A cewarsa, hatsarin ya haifar da firgici ga masu cinikayya da masu tafiya a yankin. LASTMA da sauran jami’an ceto sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka fitar da mutanen da suka maƙale a cikin shagon tare da kai su asibiti.

Advertisement

‎Jami’an tsaro sun kafa shinge a wurin domin tabbatar da tsari da kuma binciken yadda lamarin ya faru. An ce direban tankar ya tsere daga wurin bayan hatsarin, lamarin.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending