News
Tankar Mai Ta Yi Bindiga Sa’oi kadin Bayan Gobarar Kasuwar Katako Ta Bodija
Wata tanka makare da bakin mai ta yi bindiga, sa’o’i kadan bayan gobarar da ta lakume Kasuwar Katako ta Bodija da ke Jihar Oyo.
Tankar ta kama da wuta ne kimanin sa’a biyu bayan ziyarar da Gwamna Seyi Makinde na jihar ya kai wa ’yan Kasuwar Bodija ziyarar jaje, kan gobarar da ta yi musu mummunar barna.
Gwamnatin Tarayya ta kashe Milyan 560 wajan kwashe yan nijeriya zuwa masar a mota
Hukumar tsaron ta Karamar Hukumar Oluyole ta jihar ta ce, kafin motar ta yi bindiga, wasu mazauna yankin da suka lura wuta tana ci a karkashin motar sun ankarar da direban.
Ganin haka ne direban ya yi sauri ya sauka daga motar, a yayin da sauran mutanen da ke wurin kuma ya yi ta kansa.
Daga bisani motar ta bindigar, inda man da take dauke da shi ya tsiyaye a cikin magudana, wuta ta rika ci na tsawon lokaci.
A yayin ziyarar gwamnan, ya ba wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar tallafin Naira miliyan 25, sannan ya yi alkawarin Majailsar Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa za ta sake hanyoyin da ke cikin kasuwar.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
